Gwamna Ahmadu Fintiri na fuskantar suka biyo bayan nada mataimaka 47 da yayi

0 254

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri na fuskantar suka a shafukan sada zumunta, biyo bayan nada mataimaka 47 da yayi.

Ahmadu Fintiri ya sanar da nadin ne a ofishinsa a jiya.

Daga cikin wadanda aka nada akwai mashawarta na musamman guda biyu, manyan mataimaka na musamman guda 10, mataimaka na musamman 34 kan kafafen sada zumunta, sai kuma mataimaki na musamman kuma mai kula da bukukuwan gwamnati.

Ahmadu Fintiri ya bayyana cewa nadin na da nufin inganta ayyukan sadarwa na gwamnati da kuma karfafa huldar jama’a.

Sai dai da yawa daga cikin masu sharhi a karkashin wannan mukami sun caccaki gwamnan, inda suka nuna shakku kan dalilin da ya sa ya nada mataimaka a kafafen yada labarai masu yawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: