Gwamanatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ciwao bashin dala biliyan 2. Da miliyan 2 daga kasar Sin.
Hukumar fitar da kididdigar bashi ta kasa, tace Gwamanatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ciwao bashin dala biliyan 2. Da miliyan 2 daga kasa china a 2015.
Cikin kididdigar da hukumar ta fitar a kwanan nan, ta bayyana cewa a ranar 30 ga watan Yuni na 2015 Nijeria ta ciwo bashin da ya kai dala biliyan 1.38.
Haka zalika a ranar 31 ga watan maris an sake ciwo wani bashin daya tasamma Dala biliyan 3.40.
Hukumar ta kara da cewa bashin na kasar chinan an ciwo shine tare da yarjejeniyar kaso 2.50 na kudin ruwa, haka kuma kasar China zata gudanar da ayyukane a kasar nan da kudaden wanda zata nijeriya zata biyashi nan da shekaru 20 masu zuwa.
Hukumar ta kara da cewa anciwo bashin ne bisa ka’ida, saboda yayi daidai da tsarin dokar ciwo bashi na 2017.
Ayyukan da kasar china zata gudanar a fadin kasar nan sunhada da, farfado da hanyar jiragen kasa na kasar nan, hanyoyin masu fitulu a babban birnin tarayya abuja, da kuma daga likafar titin Abuja zuwa Keffi zuwa Makurdi.