Gobara ta tashi a ɗaya daga cikin kasuwanni mafi girma a birnin Accra na Ghana

0 67

Wata gagarumar wuta ta kama a ɗaya daga cikin kasuwanni mafi girma a Accra, babban birnin ƙasar Ghana, inda ta cinye akasarin kasuwar.

Har yanzu dai babu cikakken bayani kan abin da ya haifar da gobarar wadda ta tashi a kasuwar Kantamanto da tsakar dare.

Wasu daga cikin ƴan kasuwa sun garzaya domin kwashe kayansu, sai dai wutar ta yaɗu cikin hanzari.

Kimanin motocin kashe gobara 13 ne suka garzaya domin kashe gobarar.

Har yanzu ba a samu rahoton rasa rai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: