Gobara ta salwantar da rayukan mutane akalla 50 a jihar jigawa

0 331

Akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu da dukiyoyin su da suka kai kimanin Naira miliyan 215 a wata gobara da ta tashi a Jigawa a shekarar 2023 da ta gabata.

Daraktan hukumar kashe gobara na jiha Ibrahim Gumel ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai akan nasarorin da rundunar ta samu.

Ya ce hukumar ta amsa kiraye-kirayen kashe gobara 160 da kuma ceto mutane 45 daga sassa daban-daban na jihar.

Ya kara da cewa an ceto rayuka da dukiyoyi 250 sama da Naira miliyan 755 a shekarar 2023 a fadin jihar nan ta hanyar gobara da hadurran mota da dai sauransu. Gumel ya shawarci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen yin amfani da wuta ko kuma wutar lantarki, musamman a lokacin sanyi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: