Gobara ta salwantar da daruruwan gidaje a Afirka ta Kudu

0 357

Daruruwan gidaje ne suka salwanta sakamakon wata gobara da ta tashi a wata unguwar matalauta da ke birnin Durban mai tashar jiragen ruwa a Afirka ta Kudu.

An samu mutum guda da ya mutu a gobarar da ta tashi a hanyar Kennedy da sanyin safiyar jiya, sai dai ana fargabar a samu karin gawarwaki.

Hotuna da bidiyo sun nuna gine-gine suka tarwatse a cikin wata kasuwa.

Kawo yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

Sai dai wasu shaidun gani da ido sun ce lamarin ya fara ne lokacin da wasu mutane biyu da sukayi shaye-shaye suka fara samun sabani a tsakanin su. Wani mai magana da yawun kungiyar agaji ta Red Cross a Afirka ta Kudu ya bayyana lamarin a matsayin Iftila’I ya kuma yi kiyasin cewa akwai yuwuwar rushewar gidaje kusan 1,000, tare da raba mutane kusan 3,000 da matsugunan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: