Gobara ta Kashe Mutum 38 a Mexico.

0 199

Akalla mutane 38 ne suka mutu a wata cibiyar kula da bakin haure da ke kasar Mexico a wata gobara da jami’ai suka ce ta fara ne a lokacin wata zanga-zangar nuna adawa da korar bakin haure.

Yawancin wadanda abin ya shafa sun taso ne daga nahiyar Amurka ta tsakiya da ta kudu suna kokarin zuwa Amurka.

Gobarar da ta tashi a ginin da ke wani birnin kan iyaka ta tashi ne da misalin karfe 10 na dare a agogon kasar.

Ana samun kwararowar mutane a birnin a ‘yan makonnin nan.

Da yawa sun nufi kan iyakar Amurka da fatan samun kawo karshen wani kuduri da ke bai wa gwamnatin Amurka ikon gaggauta korar bakin haure da ke kokarin tsallakawa kan iyakarta.

Shugaban kasar Mexico Andrés Manuel López Obrador ya ce bakin haure sun cinnawa katifu wuta. Hotuna daga wajen sun nuna gawarwakin mutane cikin jakankuna da aka jere a waje a gefen titin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: