Gidan Ajiyar Kayan Tarihin Berlin Na Shirin Maida Wasu Sassake-sassake Najeriy

0 234

Karin gidajen adana kayan tarihi a fadin kasashen Turai sun fara duba hanyar maida kayayyakin tarihin da suka kwaso daga wasu wurare.

A wani mataki na ban mamaki, Humboldt Forum, wani sabon gidan adana kayan tarihi a Berlin mai dauke da tarin kayayyakin tarihin da ba na Turai ba, ba zai nuna sassake-sassaken tarihin da ake kira Benin Bronze ba na Najeriya, wadanda wasu da yawa suka yi zargin cewa an kwaso a matsayin ganima daga yammacin Afrika a karni na 19. Maimakon haka, ko dai za a baje kolin makamantansu ko kuma ba za a jera su ba, a cewar daraktan gidan, Hartmut Dorgerloh, ranar Litinin.

Ta yiwu ma wadannan kayayyakin tarihin ba za a sake ganinsu a gidan adanar na Jamus ba domin rahotannin sun bayyana cewa gidan tarihin na Hamboldt Forum ya fara shirin neman maida kayayyakin Najeriya. A cewar kafar yada labaran Jamus ta Suddeutsche Zeitung, Andreas Gorgen, babban daraktan cibiyar raya al’adu a ma’aikatar harkokin wajen Jamus, ya gana da shugabannin Najeriya don tattauna yiwuwar maida kayayyakin gida.

Dorgerloh ya ce ya na sa ran gidauniyar raya al’adu ta Prussia, wacce ke kula da gidajen adana kayan tarihin Berlin, za ta yanke shawara kan yiwuwar maida kayayyakin Najeriya nan da karshen shekarar nan.

“A iya saninmu a yau, wadannan sassake-sassaken tarihin na Najeriya ba bisa ka’ida aka samo su ba, a cewar Dargerloh a wata sanarwa. Ya kuma ce ya yarda dole ne a sake maida kayayyakin.”

Wannan labarin na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da kwararre a fannin ilimi Benedicte Savoy ya yi korafin cewa, gidan kayan tarihin Humboldt na shirin baje sassake-sassaken na Najeriya, wadanda a baya aka nuna su a gidan kayan tarihin Ethnological na Berlin.

Benin Bronze dai wasu sassake-sassake ne da dakarun Birtaniya suka dauke daga masarautar Benin a shekarar 1897, inda a yanzu ake kira Najeriya. An barbaza kayayyakin tarihin zuwa cibiyoyin Turai dabam-dabam, inda galibinsu suka kare a gidan ajiyar kayan tarihin Birtaniya da ke London.

Leave a Reply

%d bloggers like this: