Gidaje sama da 100 ne suka rushe sakamakon wani ruwan sama da guguwa da aka sheka a Ƙaramar hukumar Kaugama

0 174

Gidaje sama da 100 ne suka rushe yayinda dukiyoyi masu tarin yawa suka salwanta sakamakon wani ruwan sama da guguwa da aka sheka a Ƙaramar hukumar Kaugama

Tuni dai mazauna garin Kaugaman suke alhinin asarar gidaje da dukiyoyin da suka yi sanadiyyar mamakon ruwan mai haɗe da iska mai ƙarfi.

Musa Kaugama, wanda iftila’in ya rutsa da shi, ya ce gidansa mai ɗaki biyu ya ruguje, kuma ya  rasa komai sai ‘yan kayan da ba sa cikin ɗakunan

Shima Ali Haruna Kaugama, wani mazaunin unguwar da abin ya shafa, ya bayyana cewa ɗakinsa mai ɗaki uku ya lalace sosai. Garba Musa Yalo Kaugama, mazaunin Unguwar Gabas, ya  ce gidansa mai ɗaki biyu ya lalace gaba ɗaya, kuma duk kayansa sun lalace

Leave a Reply

%d bloggers like this: