Shugaban Karamar Hukumar, Hudu Babangida Dambazau wanda ya bayyana haka ga manema labarai a garin Gantsa, ya ce garuruwan da ambaliyar tafi kamari sune, Gantsa da Shawu da Buji da Matikir da Tsamfau da kuma Kukuma.
Babangida Dambazau wanda ya sami wakilcin mataimakin sa, Ahmed Zubairu, ya ce kayayyakin amfanin gona da suka lalace sun hadar da gero da dawa da wake da rogo da kuma shinkafa.
- Obasanjo ba shugaban da za a yi koyi da shi bane – Gwamnatin Tarayya
- Aƙalla ‘yan ƙasar Nijar 300 ne ake zargin hukumomin Libiya sun tsare
- Mutum 7 sun mutu yayin zanga-zangar bayan zaɓe a Mozambique
- Da yiwuwar Amurka ta fitar da hannunta daga yaƙe-yaƙen ƙasashen ƙetare
- Ƙungiyar dillalan man fetur ta cimma matsaya da Dangote kan sayen man fetur
Ya kara da cewa ambaliyar ta lalata hanyar da ta tashi daga Gantsa zuwa Tsamfau.
A jawabin sa, mai magana da yawun al’ummomin da ambaliyar ta shafa, Nazifi Garba ya roki gwamnatin tarayya da ta jiha da kuma ta karamar hukuma da sauran masu hannu da shuni su kai musu daukin gaggawa.