George Akume ya bukaci ‘yan Najeriya da su kwantar da hankulansu duk da kalubalen da ake fuskanta

0 193

Sakataren gwamnatin tarayya Sen. George Akume, ya bukaci ‘yan Najeriya da su kwantar da hankula duk da kalubalen da ake fuskanta na tattalin arziki.

Akume ya bayyana haka ne a Abuja ranar Alhamis yayin da yake jawabi ga shuwagabannin kungiyar Kiristoci ta Najeriya in da yace shugaban kasa Bola Tinubu na kokarin inganta tattalin arziki.

Ya ce gwamnati mai ci ta karbi mulki ne a lokacin da tattalin arzikin kasar nan ke cikin mawuyacin hali yana mai cewa, ana gudanar da gagarumin garambawul.

Ya ce gwamnati ta dauki matakai da dama don magance matsalolin da ake fama da su a halin yanzu, ciki har da daukar matakan gaggawa wajen aiwatar da ayyukan jin kai.

Ya ce gwamnati ta kuma dauki wasu matakai na tallafawa a sassa daban-daban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: