Ganduje Zai Share Hawayen Daliban Kano Dake Karatu A Kasashen Waje

0 289

Gwamnatin jihar Kano ta saki kudi sama da Naira Biliyan 2 domin biyan basussukan da ake bin daliban jihar dake karatu a jami’ar El-Razi a Kasar Sudan.

An ciwo bashinne zamanin mulkin tsohon gwamna, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Gwamna Abdullahi Umar ganduje ne ya fadi haka lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kwamitin amintattu na jami’ar, Farfesa Ibrahim Gandur, a gidan gwamnatin Kano.

Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta biya sama da kashi 80 cikin 100 na basussukan da ake bin daliban jihar a kasashen Cyprus, da Masar da Indiya, wanda suma aka gada daga gwamnatin data gabata.

Gwamnan ya kara da cewa, gwamnatinsa ta biya sama da Naira Miliyan 300 ga jami’ar Cyprus domin bawa daliban da gwamnatin ta dauki nauyi, dama su kammala karatunsu.

Daga nan sai ya kalubalanci wadanda ke jawo siyasa a maganar ilimi, inda yace wannan halayyar bazata amfani jihar da kasa gabadaya ba.

Tunda farko, Farfesa Ibrahim Gandur, yace sun zo Kano ne domin nuna jin dadinsu akan danganta mai kyau dake tsakanin gwamnatin jihar da jami’ar, shekara da shekaru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: