Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga ƴan kasa su ƙara haƙuri da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu duk da yanayin da ƙasar ke ciki na wahalar rayuwa.
Ganduje ya bayyana haka ne a saƙonsa na Kirsimeti da sakataren watsa labaransa, Edwin Olofu, ya fitar, inda ya bayyana ce wa tattalin arzikin ƙasar zai inganta a 2025. A cewar sa tuni dai an fara ganin sakamakon gyare-gyaren.