Ganduje ya bukaci kotu da ta dakatar da hukumar EFCC kan gayyato shi ko gudanar da bincike a kan bidiyon dala

0 552

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci wata babbar kotu a jihar da ta dakatar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, gayyato shi ko gudanar da bincike a kan bidiyon dala.

Hotunan bidiyon da jaridar Daily Nigerian ta wallafa a shekarar 2018, sun nuna yadda tsohon gwamnan ke karbar makudan kudade da ake zargin cin hanci ne daga hannun wani dan kwangila.

Yayin da gwamnan ya yi fatali da faifan bidiyon, daga baya majalisar dokokin jihar ta kafa wani kwamiti da zai binciki zargin.

Har yanzu dai kwamitin bai mika rahotonsa duk da an kaddamar da sabuwar majalisar dokokin a ranar Talata.

Sai dai a karar da ya shigar a jiya, Abdullahi Umar Ganduje, ta hanun tsohon babban lauyan gwamnatin jihar Kano, ya bukaci kotun da ta hana hukumar yaki da cin hanci da rashawar gudanar da bincike a kansa har sai an yanke hukunci tsakaninsa da Jafaar Jafaar, mawallafin jaridar ta Daily Nigerian.

Leave a Reply

%d bloggers like this: