Gamantin tarayya tana bukatar Naira Tiliyan 55 domin cike gibe karancin gidaje a Najeriya

0 124

Gamantin tarayya ta bayyana cewa, a halin yanzu tana bukatar Naira Tiliyan 55 domin cike gibe karancin gidajen da ake fama da shi a cikin shekara 10 masu zuwa.

Ministan gidaje da bunkasa birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa ne, ya bayyana haka a Abuja a yayin taron manema labarai abikin cikar ministan shekara daya a kan karagar mulki.

Ya ce, a lokacin da suka dare karagar mulki shi da karamin Minista, Abdullahi Gwarzo, sun samar da tsare-tsare na bunkasa shirin samar da gidaje masu saukin kudi daidai da manufar Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya ce wannan na da muhimmanci domin ‘yan Nijeriya su samu karin damar samun gidaje masu saukin kudi, wanda hakan zai taimaka wajen samar da walwala da kuma ci gaban tattalin arzikin kasa.

Ya kuma ce, domin cike gibin karancin gidaje a kasar nan, Nijeriya na bukatar a samar da akalla gidaje dubu 550,000 a duk shekara, nan da shekaru 10 masu zuwa, inda ake sa ran kashe kudi naira tiliyan 5.5 a duk shekara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: