Gagarumar gobara ta tashi a babbar kasuwar Funtua

0 248

Gobara ta tashi a babbar kasuwar Funtua da ke jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne tun da misalin karfe biyu na daren ranar Juma’a.

Ganau sun ce gobarar, wadda kawo yanzu ba a san dalilin tashinta ba, ta faro ne daga bangaren da ake sayar da gwanjo na kasuwar.

Wasu da suka ga yadda wutar take ci, sun ce an yi asarar kayayyaki na miliyoyin naira.

Hotunan da aka rika watsawa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda wutar take yin rimi.

Ya zuwa yanzu hukumomi ba su yi karin bayani game da tashin gobarar ba.

Sai dai wannan lamari na faruwa ne makonni kadan bayan tashin wata gobara a birnin Katsina, wadda ta lashe kayayyakin miliyoyin naira.

Leave a Reply

%d bloggers like this: