Babban alkalin Jihar Katsina, Mai shari’a Musa Abubakar Danladi, ya bayar da umarnin sakin fursunoni 185 daga gidajan yarin da ke fadin jihar, wani bangare na dakile yaduwar cutar COVID19 wajan ragewa cunkosan jama’a.
Cikin sanarawar da bababan magatakardar jihar Katsina, Alhaji Kabir Shu’aibu ya sanyawa hannu kuma ya rabawa manema labarai a jihar katsina, yace sakin fursunonin ya biyo bayan umarnin cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta najeriya NCDC, da kuma shugaban alkalin alkalan Najeriya Muhammad Tanko.
A wani labarin kuma gwamnatin jihar ta Katsina ta fara bincike gida gida nay an jihar da suka dawo daga jihar legas ko Abuja ko kuma wasu jihohin da aka samu rahoton bullar cutar COVID19.
Shugaban kwamitin karta kwana kan cutar COVID19 a jihar katsina kuma kwamishinan yada labarai Alhaji Haddi Muhammad ya shine ya fitar da sanarwar hakan.