Fursunoni 12 sun tsere daga gidan yari a jihar Kogi

0 46

Aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere baya sun fasa wani gidan yarin gwanmatin Najeriya da ke garin Kotonkarfe a jihar Kogi.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ƙara da cewa tuni sun sake kama fursuna ɗaya daga cikin waɗanda suke tsere ɗin.

Gwamnatin Kogi ta ce za ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da jami’an tsaro domin gano yadda fursunonin suka samu nasarar tserewa a safiyar ranar Litinin.

Kwamishinan ya bayyana lamarin da abin takaici, “sannan yadda fursunonin suka iya tserewa ba tare da barin wata alama ba abin tambaya ne. Dole a gudanar da bincike mai zurfi, sannan a kamo fursunonin da suka tsere, sannan a gano waɗanda suke da hannu,” in ji Fanwo.

Leave a Reply