Fiye da mutane 40 ne suka mutu, 58 suka Jikkata a haɗarurruka 5 da suka faru a Jihar Bauchi

0 331

Hukumar Kiyaye Afkuwar Hadura ta Kasa ta ce kimanin mutane 40 ne suka mutu, yayin da 58 kuma suka Jikkata a hadarurruka 5 da suka faru a cikin Satittika 3 na suka gabata a Jihar Bauchi.

Hukumar ta ce hakan ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da kuma tafiyar dare.

Shugaban Hukumar Kiyaye Afkuwar Hadura ta Kasa shiyar Jihohin Borno da Yobe da kuma Bauchi, Mista Rotimi Adeleye, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake taron manema labarai.

Mista Rotimi ya bayyana damuwa bisa yadda ake samun asarar rayuka a sanadiyar hadarirrikan.

A cewarsa, cikin makonni 3 mutane 40 ne suka mutu a manyan hanyoyin, inda kuma mutane 58 suka raunata.

Shugaban ya bukaci Direbobi su rika tuka motocin su cikin kwarewa da nutsuwa domin rage yawaitar hadarirrikan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: