Fiye da manoma dubu 1 da 178 daga kananan hukumomi 13 na jihar Jigawa wayanda ambaliyar ruwa da COVID-19 suka shafa zasu sami tallafi na musamman
Fiye da manoma dubu 1 da dari 178 daga kananan hukumomi 13 na jihar Jigawa, wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a bara, za su ci gajiyar shirin IFAD na samar da ayyukan yi da wadatar abinci.
Tallafin ya hada da samar da kayan aikin gona ga manoman da ambaliyar ruwa da COVID-19 suka shafa domin inganta nomansu na rani.
Jami’in raya aikin gona na IFAD, Yahya Buba ne ya bayyana hakan yayin da yake raba taki da maganin kwari ga manoma 90 na karamar hukumar Kafin Hausa.
Ya yi kira ga manoma da su yi amfani da tallafin don cimma burin da aka sanya a gaba, sannan ya yabawa gwamnatin jiha bisa tallafin da ta saba bayarwa don samun nasarar shirin.
A nasa jawabin, mataimaki na musamman ga gwamna Badaru kan shigar da al’umma harkokin gwamnati, Hamza Mohammed Hadejia, ya tabbatar da kudirin gwamnatin jiha na inganta aikin gona a jihar Jigawa bisa tsarin Gwamnatin Tarayya.