Femi Gbajabiamila ya musanta ware masa makudan kudade daga cikin kasafin kudin shekarar 2024

0 230

Shugaban ma’aikatan  fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, ya musanta labarin da ake yadawa a yanar gizo cewa an ware masa makudan kudade daga cikin kasafin kudin shekarar 2024 domin gyara gidan sa.

Ana ta rade-rade musamman a kafafen sada zumunta na zamani, kan cewa an ware kudi kimanin Bilyan 10 daga cikin kasafin kudin shekarar 2024 domin shugaban ma’aikata na fadar shugaban ya gyara gidan sa, da kuma karin Naira Bilyan 10.1 domin siyan kayayyakin amfanin na’ura mai kwakwalwa.

Shugaban ma’aikatar na fadar shugaban kasa yace ba’a ware masa komai ba daga cikin kasafin kudin shekarar 2024 domin ya gyra gidan sa, inda yace yana zaune ne a gidan sa na kashin kan sa.

Ya bayyana cewa kudaden da aka Ambato an ware su ne domin gyra gidan fadar shugaban kasa da mataimakin sa dake Barikin Dodan  a Jihar Legas.

Tsohon kakakin majalisar wakilan ya kara da cewa daga cikin abubuwan da za’a gyra akwai sashen sadarwa na zamani na fadar shugaban kasa, da kuma ababan hawa na fadar shugaban kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: