Félix Tshisekedi ya lashe zaɓen shuagaban kasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

0 376

An bayyana Shugaba Félix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaɓen shuagaban Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

‘Yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaɓen a matsayin na gangan suna neman a shiga zagaye na biyu.

Shugaban ya yi nasara ne da kashi 73 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, inda Moise Katumbi ya zo na biyu da kashi 18 cikin 100, a cewar hukumar zaɓen kasar.

Zaɓen na ranar 20 ga watan Disamba ya gamu da matsalolin kai kayan aiki.

Sai da aka shiga rana ta biyu ana kaɗa ƙuri’a a wasu yankunan ƙasar.

Kusan biyu cikin uku na rumfunan zaɓen ƙasar ba su buɗe da wuri ba, yayin da kashi 30 cikin 100 na na’urorin kaɗa ƙuri’a suka gaza yin aiki a ranar farko ta zaɓe, a cewar wata ƙungiya mai sa ido.

Miliyoyin mutane sun sha jira a kan layi kafin su kaɗa ƙuri’unsu, inda wasu kuma suka haƙura suka koma gida. Za a rantsar da Félix Tshisekedi a wa’adin mulki na biyu a watan Janairu da muke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: