farashin kayayyaki sun kara hauhawa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata – NBS

0 368

Hukumar Kididdiga Ta Kasa (NBS), ta ce farashin kayayyaki sun kara hauhawa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma rabon da a ga hakan tun a shekarar 1996.

Nijeriya dai na fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi da sauran nau’ikan kayayyakin amfanin yau da kullum.

A rahoton  Hukumar NBS da ta fitar, ta ce an samu karin hauhawar farashin kayayyaki a watan Nuwamba da kashi 0.87 cikin 100, idan aka kwatanta da na watan Oktoban da ya gabata. Hauhawar farashin kaya a Nijeriya yanzu ya haura kashi 27.33 cikin 100 zuwa kashi 28.20 ciki 100, kuma rabon da a shiga irin wannan yanayi na tashin farashin kayayyaki tun 1996.

Leave a Reply

%d bloggers like this: