Faransa za ta rufe ofishin jakadancinta a Nijar, inda ake nuna kyama ga Faransawa tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yuli.
Hakan ya sanya ficewar ma’aikata bayan kai wani hari lamarin da ya kawo cikas wajen gudanar da aiki a ofishin.
Dangantaka tsakanin Nijar da kasar Faransa ta yi tsami bayan da sojoji suka hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum a juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli. Dakarun Faransa da ke da hedkwata a Nijar a wani bangare na yaki da masu ikirarin Jihadi zai kammala janyewarsu a wannan watan.