Wani gungu da ya kunshi shugabannin manyan asibitoci da cibiyoyi kula da gajiyayyu a Faransa, ya yi gargadin cewa kasar na daf da sake fadawa zango na uku na annobar covid 19 da zai iya kasancewa mafi muni, la’akari da yadda ake samun karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar a kowace rana.
Duk da irin matakai da mahukunta suka dauka domin rage cunkoso da kuma tarukan jama’a, yanzu haka asibitoci na ci gaba da karbar dubban mutane da suka kamu da cuta a sassan kasar, lamarin da ya haifar da fargaba dangane da daukar sabbin matakai a cikin kwanuka masu zuwa.
To sai dai duk wannan gargadi da shugabannin asibitoci da kuma cibiyoyin kula da gajiyayyun suka fitar, shugaban kasar Emmanuel Macron wanda ke zantawa da jaridar Le Journal du Dimanche a jiya, ya ce kawo yanzu gwamnati ba ta yanke shawarar daukar sabbin matakai na killace jama’ar kasar ba.
Shugabannin asibitocin da kuma cibiyoyyin kula da gajiyayyu 41 ne suka yi gargadin cewa, lura da adadin mutanen da ke kamuwa da cutar mai shake numfashi a kowace rana, ba mamaki annobar ta kai matsayi mafi kololuwa tamkar dai irin wadda da aka gani a watan nuwamban bara.
Annobar dai ta fi tsananta ne jihohi 5 na kasar ciki har da birnin Paris, inda tsakanin ranar 15 zuwa 21 ga watan Maris da muke ciki aka samu karuwar akalla 31% na kananan yara ‘yan kasa da shekaru 14 da suka kamu da ita.