Fannoni biyu da suka samu kaso mafi yawa a kasafin kuɗin Jigawa 2019

0 453

Gwamna Muhammad Badru Abubakar ya gabatar da kudirin dokar kasafin kudin shekara mai zuwa na sama da Naira miliyan dubu dari da hamsin da biyu da miliyan dari tara ga Majalisar dokokin jihar Jigawa domin amincewa.

Haka zalika gwamnan ya gabatar da kudirin kasafin kudin kananan hukumomin jihar 27 na Naira miliyan dubu sabain da biyu da miliyan dari takwas.

Muhammad Badru Abubakar ya yi bayanin cewa kasafin kudin zai maida hankali wajen kammala ayyukan da ake gudanarwa da kuma sabbin ayyuka a shekara mai zuwa.

Ya yi bayanin cewa ilimi da kiwon lafiya su ne suka samu kaso mafi tsoka na kashi talatin da bakwai na daukacin kasafin kudin.

Daga nan ya yi fatan wakilan Majalisar zasu duba da kuma amincewa da kasafin kudin akan lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: