Falasɗinawa sun fara komawa gidajensu da yaƙi ya rugurguza a birnin Khan Younis da ke gabashin Gaza
Falasɗinawa sun fara komawa gidajensu da yaƙi ya rugurguza a birnin Khan Younis da ke gabashin Gaza bayan da dakarun Isra’ila suka janye daga yankin.
Farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta ƙasa ya ragargaza gine-ginen yankin.
Ministan tsaron Isra’ila ya ce sojojin sun bar yankin ne domin sake ɗauro sabuwar damarar yaƙar Hamas a Khan Younis ɗin da Rafah, inda Falasɗinawa sama da miliyan ke gudun hijira. Khan Younis dai gari ne da aka ɗai-ɗaita a kudancin Gaza bayan da Isra’ila ta sanar cewa ta soma janye sojojinta daga birnin.