Fadar shugaban kasa ta bukaci Atiku da ya kawo hanyar magance matsalolin da suka dabaibaye kasar

0 270

Fadar shugaban kasa ta bukaci dan takarar shugaban kasa na zaben daya gabata a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da ya kawo hanyar magance matsalolin da suka dabaibaye kasar wanda ta fi wanda gwamnati ke yi.

Tace kawo hanyoyin warware matsalar ita ce mafita kan halin da ake ciki maimakon dorawa shugaban kasa Bola Tinubu alhakin kasa magance matsalar.

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai da tsare-tsare Bayo Onanuga  yayi wannan kira a wata sanarwa daya fitar jiya a Abuja.

Bayo Onanuga yace shugaba Tinubu na fuskantar matsin lamba kan tsarin tattalin arziki tun lokacin da ya karbi mulki a ranar 29 ga watan mayun bara.

Yace batun cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu yay na daya daga cikin hanyoyin da  dukkan jam’iyyun siyasa suka ayyana a matsayin hanyar magance matsalar tattalin arziki a kasa. Haka kuma ya bukaci yan najeriya da masu zuba jari da su gaskata yunkurin gwamnatin tarayya na bunkasa cigaban kasa da yan kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: