Shugaban majalissar Dattawa ta kasa Femi Gbajabiamila, yace Gwamnan Jihar Lagas Babajide Sanwo-Olu yace jihar tana bukatar Naira Tiriliyan Daya domin a sake gina wajen da masu zanga-zangar #EndSARs suka rushe.
Gbajabiamila ya fadi haka a lokacin da yake hira da yan jaridu a majalissar bayan ziyarar gani da ido kan wuraren da masu zanga zangar suka barnatar a birnin Lagas.

- Majalisar Dokokin Legas ta sake zaɓen Obasa a matsayin kakakinta
- An yi garkuwa da wani ɗansanda a Abuja
- Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da tallafin karatu da ya kai Naira biliyan 2.22 ga dalibai 890
- Kungiyar NANS ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin Najeriya
- Kotun ta yi watsi da bukatar hana jami’an gwamnati tafiya kasashen waje don neman magani
Ya ce majalissar zatayi duk mai yuwuwa domin biyan diyya ga wadanda rikicin ya rutsa da su, da suka hadar da jami’an yan sanda da suka rasa rayukansu.
Ya kuma bukaci matasa da kwantar da hankulansu, domin dawo da zaman lafiya, tare da bayyana kwarin gwiwarsa kan hadin kan kasa.