Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 23 ga watan Oktoba domin sauraren karar da tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke ta shigar a gabanta na kalubalantar kwace kadarorinta da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta yi.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya tsayar da ranar Laraba bayan lauyan Diezani, Benson Igbanoi, da lauyan hukumar EFCC, MD Baraya, sun daidaita ayyukansu.
Shugaban Hukumar EFCC da aka dakatar, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa an kwato $153m da wasu kadarori sama da 80 daga hannun Diezani.
Ko da yake hukumar ta EFCC ta ce Diezani ta tsere zuwa Birtaniya a shekarar 2015 a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan inda ta rike mukamin minista, don gudun kada a kama ta, Diezani ta ci gaba da cewa taje kasar Birtaniya ne domin ayi mata maganin kansar.
A cikin karar da ta shigar ta hannun lauyanta Mike Ozekhome, SAN, Diezani ta kuma bukaci kotun da ta yi watsi da karar da aka yi mata a ranar 24 ga Yuli, 2020.
Ta zargi hukumar EFCC da boye gaskiya don samun sammacin benci, inda ta ce ba a yi mata adalci ba kafin EFCC ta tura kotu ta kwace kadarorinta ga gwamnatin tarayya. Hukumar ta EFCC dai ta ce an bi dukkan ka’idojin da doka ta shimfida, inda ta kara da cewa ba a ajiye ko daya daga cikin wadannan kadarori ba da aka yi watsi da su.