EFCC ta kama wani mutum bisa zargin almundahanar taki ta Naira miliyan 108

0 54

Hukumar EFCC ta gabatar da wani mutum mai suna Sanusi Hashim bisa zargin almundahanar taki ta naira miliyan 108.

An gabatar da Hashim ne a babbar kotun tarayya da ke Zarian Jihar Kaduna a gaban Mai shari’a Kabiru Dabo kan zargin rashawa, wanda ya saɓa da sashe na 293, wanda kuma ya cancani hukunci a ƙarƙashin sashe 294 na kundin laifuka.

An zarge shi ne da karɓar naira miliyan 108 daga Ahmad Mohammad Liman da Bashiru Mohammad domin ya kawo musu taki, amma ya ƙi kai musu, zargin da ya musanta. A ƙarshe Mai shari’a Dabo ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 10 ga Fabrairun 2025, sannan ya buƙaci a ajiye wanda ake ƙara a kurkuku.

Leave a Reply

%d bloggers like this: