Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta kama tare da tsare shugaban hukumar zuba jari ta kasa Halima Shehu.
Manema labarai sun ruwaito cewa kamen nata na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umurnin dakatar da ita, saboda zargin almundahanar kudaden da suka kai kimanin naira Biliyan 17 daga asusun Hukumar zuwa wasu asusun a cikin mako guda.
An zargi Halima da bayarda umurnin fitar da kudaden Biliyoyin Naira daga hukumar ta ba tare da izinin shugaban kasa ba.
An bayyana cewa jami’an hukumar ta EFCC sun samu nasarar kamata ne da misalin karfe 8 na daren jiya Talata inda aka wuce da ita domin amsa tambayoyi.