EFCC na ci gaba da yi wa tsohon gwamnan na CBN tambayoyi

0 247

Hukumar Yaki da yi wa Tatalin Arzikin kasa Ta’annati (EFCC) ta tsare tsohon gwamnan Babban Bankin kasa, Godwin Emefiele, bisar zargin tafka almundahana a yayin da yake rike da shugabancin babban bankin.

EFCC ta kama Emefiele, ƙasa da sa’a guda bayan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sake shi.

Rahotonni ne cewa EFCC na ci gaba da yi wa tsohon gwamnan na CBN tambayoyi, a shalkwatar hukumar da ke Abuja.

EFCC na tuhumar Emefiele kan zarge-zargen saɓa ƙa’idar aiki a lokacin da yake gwamnan CBN.

Cikin watan Yuni ne dai hukumar DSS ta kama Emefiele jim-kaɗan bayan shugaban ƙasar Bola Tinubu ya dakatar da shi daga aiki. Sake kama Emefiele na zuwa ne kasa da sa’o’I 48 bayan tsohon shugaban hakumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC Abdulrasheed Bawa, ya shaki iskar yan ci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: