ECOWAS za ta yi duk abin da ya dace don maido da dimokuradiyya a Nijar

0 461

A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaba Bola Tinubu da mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris da sakatare janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres sun bayyana goyon bayansu ga kokarin Najeriya na maido da tsarin mulkin jamhuriyar Nijar.

Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman da sadarwa da dabaru Dele Alake ya fitar ta bayyana cewa, shugabannin biyu sun kuma yabawa shugaban Najeriyar wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS da ya jagoranci yunkurin samar da zaman lafiya a Nijar. Bayan da wasu sojoji daga cikin masu tsaron fadar shugaban kasa suka yi yunkurin tsige shugaba Mohamed Bazoum a ranar Laraba 26 ga Yuli, 2023.

Ba tare da bata lokaci ba Shugaba Tinubu ya yi watsi da barazanar dimokuradiyya a kasar, inda ya tura wata tawaga mai karfi da za ta tattauna da dukkan bangarorin da nufin maido da tsarin mulki a Nijar.

Yayin da take yin alkawarin tallafawa dimokuradiyya a Afirka ciki har da yankin yammacin Afirka, Harris ta kuma ce Amurka za ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta’addanci.

Mataimakiyar shugaban na Amurka ta yi magana game da bukatar Afirka, ciki har da Najeriya ta rungumi canjin makamashi.

Shugaba Tinubu ya godewa Harris bisa wannan kiran da kuma kalamanta na karfafa gwiwa kan kokarin da aka yi kan tattalin arzikin kasar, amma ya kara da cewa “abubuwan da ke faruwa a jamhuriyar Nijar na sanya rudani.”

Ya ce kungiyar ECOWAS da ke karkashin sa za ta yi duk abin da ya dace don maido da dimokuradiyya a Nijar, tare da la’akari da goyon bayan Amurka.

A kan Najeriya, shugaba Tinubu ya bukaci karin jarin kamfanoni masu zaman kansu, inda ya bukaci Amurka da ta jagoranci wannan fanni.

A lokacin da yake magana da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Guterres, Shugaba Tinubu ya ce yana yin duk mai yiwuwa don ganin an sasanta rikicin Nijar.

Yayin da yake bayyana fatan cewa har yanzu za a iya sauya halin da ake ciki a Nijar din, ya ce kungiyar ECOWAS za ta bukaci goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya domin maido da dimokuradiyya da gina cibiyoyi a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: