ECOWAS sun sanya takunkumin hana tafiye-tafiye da hana amfani da kudaden asusun ajiya na shugabannin juyin mulkin Guinea

0 217

Shugabannin Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) sun sanya takunkumin hana tafiye-tafiye da hana amfani da kudaden asusun ajiya na shugabannin juyin mulkin Guinea da iyalansu.

Ana sa ran takunkumin zai kara matsin lamba ga gwamnatin mulkin soji don maido da tsarin mulki.

An ba da sanarwar yanke hukuncin ne bayan wani taron koli na musamman da aka gudanar a Accra, Ghana.

Kazalika ECOWAS na son sojojin su gudanar da zabe cikin watanni shida kuma ta dage cewa babu wani daga cikin shugabannin sojoji da za a bari ya tsaya takara a zaben.

Shugabannin duk da haka sun nuna aniyarsu ta tallafawa kasar ta hanyar tsarin rikon kwarya.

Sun yi kira ga Kungiyar Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya, da takwarorinsu na kasa da kasa da su taimaka wajen aiwatar da takunkumin tafiye-tafiye da takunkumin kudi kan shugabannin mulkin soji da iyalansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: