Duk kilomita 1 na aikin hanyar gabar ruwan Legas zuwa Kalaba zai laƙume ₦4Bn – David Umahi

0 213

Ministan Ayyuka na Kasa, David Umahi, ya ce duk kilomita ɗaya na aikin hanyar gabar ruwan Legas zuwa Kalaba da ake yi zai laƙume Naira biliyan huɗu.

Ya bayyana haka ne a wani martani da ya yi wa Atiku Abubakar, kan cewar aikin kowace kilomita na titin na laƙume Naira biliyan takwas.

Umahi, ya ce aikin hanyar ya kai kimanin kilomita 700 wanda aƙalla zai laƙume Naira tiriliyan 2.8.

Ya musanta zargin da ake yi na cewa ba abi ƙa’idojin da suka dace ba wajen bayar da aikin.

A makon da ya gabata ne, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku ya soki matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya ɗauka na bayar da kwangilar aikin ga kamfanin Gilbert Chagoury’s Hitech ba. Atiku ya yi zargin cewar ba a bai wa wasu ’yan kwangila dama domin su gabatar da buƙatarsu a tantance ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: