Donald Trump Yace Bai Aikata Laifin Komai Ba.

0 177

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya fadawa kotu cewa bai aikata laifin komai ba a tuhume-tuhumen da aka zayyana masa.

Masu shigar da kara a birnin New York suna tuhumar Trump da aikata laifuka 34 wadanda ke da alaka da biyan wata mata mai fitowa a fina-finan batsa kudin toshiyar baki.

Dukkan laifukan sun fada ajin manyan laifuka a dokar kasa.

Ana zargin Trump ya biya Stormy Daniels dala dubu 130 don ta rufa masa asiri kan zargin neman ta da ya taba yi kafin ya zama shugaban kasa. Trump ya sha musanta wannan zargi.

Mai shigar da kara a Gundumar Manhattan a New York, Alvin Braggs
Mai shigar da kara a Gundumar Manhattan a New York, Alvin Braggs

Bugu da kari, ana zargin Trump ya yi karya wajen ba da bayanan kudaden hadahadar kasuwancinsa.

Bayanan da masu shigar da kara suka gabatar a gaban kotun, sun nuna cewa Trump ya ayyana kudin da aka biya Daniels a matsayin kudin aikin lauya, alhali ba haka ba ne.

Trump ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da aka masa.

Magoya bayan Trump
Magoya bayan Trump

Idan kotun ta Manhattan ta samu Trump da laifi a karshen wannan shari’a, hukuncin da doka ta tanada ya hada har da zaman gidan kaso.

Tuni aka ba da belinsa, ya kuma koma gidansa na Mar-a-Largo da ke jihar Florida inda ya wani dan kwarya-kwaryan taron gangami.

Da tsakar ranar Talata Trump ya mika kansa ga hukumomi inda aka gabatar da shi a gaban kotu a wani lamari da ba a taba gani ba.

Tun da safiyar ranar Talata, dandazon magoya bayansa da masu adawa da shi suka yi dafifi a kofar kotun don kallon yadda zaman shari’ar zai kaya.

Dandazon jama'a a kotun da aka gurfanar da Trump
Dandazon jama’a a kotun da aka gurfanar da Trump

Trump mai shekaru 76, shi ne tsohon shugaban Amurka na farko da ya fuskanci tuhumar aikata laifi a tarihin Amurka.

A bara ya ayyana burinsa na sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben da za a yi a 2024.

A Amurka, babu wata doka da ta hana wani da ake tuhuma ko aka samu da laifi tsayawa takarar shugaban kasa ko rike mukamin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: