Domin Cigaban Afrika Sai An Kawar Da Tsofaffi Daga Mulki – Obasanjo

0 181

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obansanjo yayi kira ga matasan Afirka da su kawar da dattawa daga shugabanci.

Obasanjo ya bukaci matasan da su tsunduma a harkokin jam’iyyun siyasa domin kwace madafun iko daga hannunsu.

Tsohon shugaban kasar ya fadi haka a jiya lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen wata tattaunawa ta bidiyon kai tsaye, domin tunawa da ranar matasa ta duniya ta bana.

Cibiyar cigaban matasa, wacce bangare ne na dakin karatun shugaban kasa na Olusegen Obansanjo dake Abekutan jihar Ogun, ta shirya tattaunawar.

An zabo mahalarta daga Najeriya da Mali da Amurka da Ghana da Kenya da Afirka ta Kudu.

A cewarsa, muddin ba dattawa aka kora daga siyasa ba, zasu cigaba da rike mukamai, suna barin matasa a iska.

Leave a Reply

%d bloggers like this: