Dole ƴanjarida da jami’an tsaro su haɗa kai domin daƙile matsalar tsaro – Rundunar tsaro

0 85

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar CG Musa ya nanata buƙatar da ke akwai na haɗin gwiwa tsakanin sojoji da kafofin watsa labarai domin magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Musa ya bayyana haka ne a wani taro da ƙungiyar ƴanjarida ta ƙasar reshen jihar Kaduna ta shirya, inda ya ce ƴanjarida na da rawar da za su taka wajen wayar da kan al’umma ta hanyar watsa labarai masu muhimmanci, da ma haɗin kan ƙasa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Janar Musa, wanda Birgediya Janar Mohammed Kanah ya wakilta, ya ce “haɗin gwiwa tsakanin sojoji da ƴanjarida na da matuƙar muhimmanci, domin aikinmu na da muhimmanci sosai wajen gina ƙasa da saita ta.

“A daidai lokacin da sojoji suke bayar da tsaro da tabbatar da tsaro, su kuma ƴanjarida su ne suke sa ido, da bin diddigi domin tabbatar ana aikin yadda ya dace. Sai dai haɗin kai tsakanin ɓangarorin biyu na fuskantar ƙalubale, ciki har da yaɗa labaran ƙarya.”

Domin magance wannan matsala, Janar Musa ya yi kira da a ƙara fahimtar juna tsakanin ɓangarorin biyu, sannan ya buƙaci a ci gaba da horar da ƴanjarida.

Leave a Reply