Kungiyar kare haƙƙin ƴan jarida ta jamhuriyar Nijar da ake kira RJDH ta bayyana matuƙar damuwarta kan yadda gwamnatin soja ta yi wa dokokin ƙasar da suka shafi aikata laifuka ta intanet.
Yanzu dai dokar ta tanadi hukunci mai tsanani kan laifukan ɓatanci da cin mutunci da aka yi ta hanyar intanet.
Kungiyar ta bayyana wannan gyaran fuskar da babban koma baya ga ƴancin ƴan jarida da kuma faɗin albarkacin baki da ka iya daƙile wa jama’a damar bayyana ra’ayoyi daban-daban.
Ƙungiyar ta RJDH ta ce hakan ya haifar da fargabar cin zarafin ƴan jaridun jamhuriyar ta Nijar.
Ƙungiyoyi da dama a jamhuriyar dai na yi wa gwamnatin soji ta Abdourahmane Tchiani kallon wadda ke kokarin rufe bakin al’ummar ƙasar.