Dokar karin haraji a kasar kenya ta jawo zanga-zanga

0 191

Yan sanda a Kenya sun yi amfani da hayaƙi mai sa ƙwalla don tarwatsa dandazon masu zanga-zangar allawadai da dokar da za ta bayar da damar ƙarin kuɗaɗen haraji.

An kama mutane da dama a Nairobi babban birnin ƙasar. Kungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun yi allawadai da matakin da ‘yan sandan suka ɗauka.

Wakilin BBC ya ce matasan Kenya da dama na bayyanawa gwamnati cewar ba za su amince da ƙarin haraji ba, sun yi arangama da hayaƙi mai sa hawaye da yan sanda suka harba, yayinda aka sanyawa wasu daga cikinsu ankwa.

Tun da farko dai gwamnatin ƙasar ta sake yin duba, inda ta kankare wasu haraje-haraje da suka haɗa da na biredi, gwamnatin ta kuma ƙara da cewar tana sane da yadda al’ummar ƙasar ke fama da tsadar rayuwa.

Tuni dai shugaba William Ruto ya ɓullo da wasu sabbin haraji da ya ce ya zama wajibi domin rage bashin da ake bin ƙasar na kusan dala biliyan tamanin da ya gada daga gwamnatocin baya

Leave a Reply

%d bloggers like this: