Daruruwan masu zanga-zanga ne suka cika titunan birnin Tunis na Tunisiya, domin matsa wa gwamnati lamba da wasu fitattun ‘yan adawa 20, waɗanda ba su ga-maciji da shugaban ƙasar, Kais Saied.
Kusan masu zanga-zanga 300 ne suka yi tsayuwar gwaman jaki dauke da tutar kasar da alluna masu dauke da alama da hotunan yan adawar da suke zargin gwamnatin kasar da daurewa.
Tun a watan Fabrairu da ya wuce ne aka kama mutanen da suka hada da manyan yan siyasa ciki har da tsaffin ministoci, yan kasuwa da jagororin kungiyoyin yan kasuwa da kuma mamallakin wani gidan radiyo mafi shahara a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, ya ce babbar jam’iyar adawa ta National Salvation Front ce ta shirya zanga-zangar.
Masu boren sun zargi shugaba Saied da tursasa ‘yan kasa da salon mulkin danniya. Kungiyoyin kare yancin dan adam na cikin gida da na duniya sun kalubalanci matakin shugaban.
A watan Yulin 2022 ne ya kori daukacin majalisar ministocinsa, tare da rushe majalisar kasar baki daya.
Sai dai shugaba Kais ya ce wadanda aka kama din ‘yan ta’adda ne, da suke barazana ga tsaron Tunisia.
- Comments
- Facebook Comments