Daruruwan Falasdinawa sun rasa ransu sakamakon harin sojojin Isra’ila a Gaza

0 291

Daruruwan Falasdinawa ne sojojin Isra’ila suka kashe a Gaza a karshen mako yayin da sojojin Isra’ila suka ba da umarnin karin yankuna a ciki da kewayen birnin Khan Younis birni na biyu mafi girma a yankin da su kaura, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Qatar, tare da taimakon Masar, ta taimaka wajen cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta na kwanaki hudu, wadda ta fara aiki a ranar 24 ga watan Nuwamba, amma aka tsawaita sau biyu.

Tsagaita bude wuta da aka yi bayan yin garkuwa da mutane, ya biyo bayan yakin da aka shafe makonni ana gwabzawa a zirin Gaza bayan mayakan Hamas sun kutsa kai kan iyakar Gaza da Isra’ila mai dauke da sojoji a ranar 7 ga watan Oktoba a wani hari.

Kafin a fara tsagaita wutar, an bayar da rahoton cewa, hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama da kuma mamayar kasa sun kashe Falasdinawa sama da 14,000, galibi mata da kananan yara, tare da tilastawa mutanen Gaza kimanin miliyan 1.7 barin gidajensu.

Darakta-janar na ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza Ismail Al-Thawabta a jiya ya shaidawa Al Jazeera cewa an kashe Falasdinawa sama da 700 a cikin sa’o’i 24n da suka gabata; daya daga cikin adadin mace-macen yau da kullum tun bayan yakin.

An ba da rahoton tashin bama-bamai masu tsanani a Khan Younis da Rafah da kuma wasu sassan arewacin kasar da Isra’ila ta kai hare-hare ta sama da ta kasa tsakanin  ranakun Asabar da Lahadi.

A wani labarin kuma, Isra’ila ta tsare Falasdinawa akalla 60 a hare-haren da ta kai cikin dare a yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, a cewar kungiyar ‘yan fursuna ta Falasdinu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: