Darasin Korona: Nijeriya zata fara zuba Makudan Kudade Don Binciken Magunguna

0 322

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sahalewa kudirin samar da cibiyoyin binciken magunguna, da bada horo a kwalejojin karatun likita 6 dake shiyyoyin kasarnan.

Bugu da kari Shugaba Buhari, ya amince da karin kudin hukumar na shekarar 2020 zuwa naira biliyan 7 da miliyan 5, sabanin naira biliyan 3 da yake a baya.

Babban sakataren hukumar TETfund, Farfesa Sulaiman Bogoro, shine ya bayyana hakan, yayin taron kwamatin amintattu na shekarar 2020 da aka gudanar a Abuja.

Yace amincewa batun ya baiwa hukumar TETFund damar gina dakunan gwaje gwajen cutuka masu yaduwa biyu a kowacce shiyyar kasarnan, abinda zai sanya hukumar ta zama gagara misali, wajen samar da cibiyoyin gwajin cutar corona a Nigeria.

Farfesa Bogoro ya kuma ce kwamatin amintattun hukumar, ya amince da zuba naira miliyan 200, domin daukar nauyin wasu jami’o’i dama hukumar NAFDAC wajen gudanar da bincike kan cutar corona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: