Darakta janar na hukumar bautar kasa NYSC Shuaibu Ibrahim a jiya alhamis a birin Uyo ya jajantawa iyalan wasu matasa masu bautar kasa guda 5 wanda suka rasa rayuwarsu a kan hanyar Abuja zuwa Abaji a ranar laraba.
Yan bautar kasar wanda yan asalin jihar Akwa Ibon ne sun kammala karatun Digiri a jamiar Uyo, sun rasu ne a wani Hadarin mota a kan hanyarsu ta zuwa sansanin horas da matasan dake Katsina.
Mista Ibrahim wanda Birgeduya ganar ne ya kuma bada umarnin sauke tutar ta NYSC zuwa kasa na tsawon kwanaki 3 domin nuna jimamin rashin matasan da suka rasa rayuwarsu.
Ya ce labarin hatsarin yayi matukar jijjaga zukatan daukacin iyalan yaran da suka tura yaransu zuwa sansanoni daban-daban a fadin kasar nan, ya kuma roki Allah ya jikansu tare da bawa iyalansu hakuri da juriya.
Daga nan ya ja hankalin sauran matasan dasu kauracewa bulaguro da dare.
Tun da farko Darakta janar Shuaibu Ibrahimya kai ziyarar ta’aziyya ga gomna Udom Emmanuel da kuma jamiar Uyo.