Darajar naira ta ci gaba da faduwa sakamakon rikicin haraji tsakanin Amurka da wasu kasashe, wanda ya haddasa fitar da kudaden hannun jari daga Najeriya.
A kokarinsa na dakile matsalar, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sayar da dala miliyan 500 a kasuwar hada-hadar kudi a makon da ya gabata.
Duk da haka, naira ta sake yin kasa inda ta fadi zuwa N1,600 a kowace dala a kasuwar bayan fage, mafi karancin darajarta cikin makonni biyar.
Masana tattalin arziki sun danganta wannan da karancin dalar Amurka da kuma rudanin da yakin harajin ke haifarwa ga kasuwannin hada-hadar kudi na duniya.