Danyen Man Nijeriya Yayi Kwantai A Kasuwar Duniya

0 209

Dillalan mai na fadi tashin neman masu sayen jiragen ruwa 55 dauke da danyen man Najeriya, bayan yaduwar cutar coronavirus ta rage bukatar man daga masu tace mai a China da Turai.

Ba a sayar da dayawa daga cikin danyen man Najeriya ba, yayin da ba a samu masu sayen kimanin rabin danyen man Angola ba, a cewar wasu dillalai biyu, wadanda suka kware a cinikayyar man Afrika ta Yamma.

A cewar kamfanin Bloomberg, kimanin kaso 70 cikin 100 na jiragen ruwa dauke da danyen mai daga Angola da Najeriya basu samu masu saye ba, koma bayan sosai akan yadda aka saba.

Kamfanin yace danyen man da ba a sayar ba, zai yi gogayya da miliyoyin gangunan danyen mai da ake shirin kai wa kasuwa wannan watan, wanda har yanzu ba a samu masu saye ba.

A cewar kamfanin na Bloomberg, Najeriya da Angola na shirin fitar da jiragen ruwa 100 makare da danyen mai a watan Afrilu, hakan na nufin yawan man da ba a sayar ba ya kai kashi 70 cikin 100.

Leave a Reply

%d bloggers like this: