Daniel Bwala mai magana da yawun Atiku Abubakar ya caccaki Hukumar EFCC

0 259

Daniel Bwala mai magana da yawun dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP a Zaben 2023, Atiku Abubakar ya caccaki Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC).

Bwala ya soki EFCC dangane da ayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

Bwala wanda ya yi wannan babatu cikin wani sako da ya wallafa shafinsa na X (Twitter) a ranar Juma’a, ya ce Hukumar EFCC nada duk wata dabara da bayanan sirri da za ta iya kama Yahaya  Bello.

Ya nanata cewa kamata ya yi jami’an EFCC su yi amfani da tsari da kuma dabarar da suka yi wajen kama tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha a shekarar 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: