Dan takarar jam’iyyar adawa Bassirou Diomaye Faye ne ke kan gaba a zaben shugaban kasar Senegal

0 280

Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Senegal na nuna dan takarar jam’iyyar adawa Bassirou Diomaye Faye ne ke kan gaba, lamarin da ya sanya magoya bayansa fita kan tituna don fara nuna murnar nasara a zaben, ko da yake babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar da ke mulki ya ce sai an gudanar da zaben zagaye na biyu ne za a iya tantance wanda yayi nasara.

Tuni dai akalla ‘yan takara 5 daga ciki 17 da ke fafatawa a zaben, suka fidda sanarwar taya Faye murna, duk da ya ke tsohon firaministan kasar Amadou Ba da ke takara a jam’iyar da ke mulki ya ce ya yi wuni mutane su fara murnar sakamakon farko na zaben.

Miliyoyin mutane ne dai suka kada kuri’ar zaben shugaban Senegal na biyar a tarihi, don zabo wanda zai maye gurbin shugaba Macky Sall da gwamnatinsa ta sha suka kan rashin samar da tsarin saukaka matsin tattalin arziki.

A cewar kafar talabijin din kasar, kashi 71 na yawan masu kada kuri’a miliyan 7 da dubu dari 3 ne suka yi zabe a kasar da ke da akalla yawan mutane miliyan 18. Sakamakon farko na zaben da aka bayyana a gidan talabijin din kasar ya nuna cewa Faye ne ke kan gaba, lamarin da ya magoya bayansa fara gudanar da bukukuwa a titunan Dakar babban birnin kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: