Dalilan da yasa tawagar lauyoyin da ke wakiltar Sheikh Abduljabbar Kabara suka janye wakilcin su

0 264

Tawagar lauyoyin da ke wakiltar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a shari’ar sabo da ake yiwa malamin, sun janye wakilcin su.

Lauyoyin da Haruna Magashi ke jagoranta, sun nemi su janye daga karar a yau a cigaba da sauraron karar a gaban Babbar Kotun Shari’a da ke Kofar-Kudu a birnin Kano.

Alkalin kotun, Ibrahim Sarki Yola, ya amince da bukatar su, bayan haka Abduljabbar ya nemi kotun da ta ba shi lokaci don samun sabbin lauyoyi.

Alkalin ya amince da rokon malamin sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Satumba.

Tun da farko, kotun ta samu rahoton lafiya daga asibitin Murtala Mohammed da asibitin masu tabin hankali na jihar Kano dake Dawanau kan lafiyar kunne da lafiyar kwakwalwar malamin. Rahotannin biyu, a cewar kotun, sun nuna cewa malamin ba shi da wata matsalar kunne ko tabin rashin hankali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: