Dalilan Da Yasa Majalisar Kasa Zata Dawo Aiki Gobe

0 216

Majalisar Wakilai ta Kasa ta sanar da shirinta na komawa bakin aiki da zaman majalisar, a ranar gobe Talata.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da magatakardan majalisar, Patrick Giwa, ya aikewa dukkan ‘yan majalisar.

Majalisar a watan Maris da ya gabata ta dage zamanta na tsawon makonni 2, a kokarin dakile bazuwar cutar corona. Daga baya ta kara wa’adin dagewar domin ta dace da dokar kulle a babban birnin tarayya.

Dangane da matakan kariya, Mista Giwa yace za a aikawa ‘yan majalisar sharuddan kare kai daga cutar corona da gwamnatin tarayya da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC suka amince da su, da karin wasu sharuddan da majalisar ta samar.

Sai dai yace ma’aikata da hadiman ‘yan majalisar zasu cigaba da aiki daga gida, kuma za a sanar da su dukkan lokacin da ake bukatarsu a wajen aiki domin wani aiki na musamman.

Leave a Reply

%d bloggers like this: